
Forex da Crypto: Halal ko Haram?
Wani tsari ne da ke sake fasalta kasuwancin kuɗi na zamani ta hanyar ɗabi'a, ingantaccen tsari, da hikimar kuɗi, domin cike giɓin da ke tsakanin neman riba da kuma gudanar da mu'amalar kuɗi bisa ƙa'ida da amana. A qarshe, Babbar manufata ita ce samar da sabon ƙarni na 'yan kasuwa, injiniyoyi, da masu tunani waɗanda za su fahimci cewa tsarin kuɗi ba kayan samar da arziki kawai ba ne; tsarin amana ne, nauyi ne, da kuma hisabi, kuma kai mai karatu yana da kyau ka sani duk abinda zaka karanta acikin wannan littafi ya kasance bincikena ne na tsawon lokaci wanda na saka hujjoji da bayanai, duk abinda ka gani na kuskure wannan daga nine kasawa ta ce a matsayina na dan adam, duk abinda yake dai kuwa daga Allah ne domin shine mai dai dai akan komi, ina kara kira ga malamai da daliban ilimi cewa wannan littafi zan iya kiransa littafin nazarin kwa kwaf da kuma abinda na fahimta na shekaru a fanni fanni na wannan kasuwa dama fannin naura mai fikira. Har yanzu ina zaune a Najeriya, yayin da nake gudanar da ayyukana a matakin duniya a mahadar binciken kimiyya, harkokin kasuwanci, da ƙirƙirar tsarin kuɗi na zamani. Yanar Gizo: www.fxlens.net